KUNGIYAR MA’AIKATAN MAI SUN SOMA YAJIN-AIKI
Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta soma yajin gama-gari saboda korar ‘ya’yanta daga aiki da ake yi.
Kakakin kungiyar PENGASSAN, Emmanuel Ojugbana, ya bayyana wa manema labarai cewa sun dauki matakin ne saboda kamfanonin man da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kan jin dadin ma’aikata.
Ojugbana ya ce, za su tattauna da ministan kwadagon Nijeriya Chris Ngige domin ya shiga tsakaninsu da kamfanonin man.
Comments