Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Rungumi Wani Mutum A Maiduguri

Wani dan kunar-bakin-wake da aka yi kokarin hana shiga masallaci ya rungumi wani mutum inda suka mutu tare a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa dan kunar-bakin-waken ya so shiga masallacin ne amma mutumin da ke binciken mutane kafin su shiga ya haska shi da cocilan.
Ganin hakan ne ya sa dan kunar-bakin-waken ya tunkare shi inda ya rungume shi suka mutu tare.
Ganau din ya ce sun ji karar bam din da ya fashe inda suka garzaya wurin, kuma sun ga gawarwakin mutanen sun yi kaca-kaca.
Wannan dai shi ne karo na uku a cikin wannan watan da 'yan kunar-bakin-wake suka tashi bam a masallatan da ke birnin.
A kwanakin baya, wata 'yar kunar-bakin-wake ta tashi bam a wani masallaci inda mutum hudu suka rasa rayukansu ciki har da wani Farfesa.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya