Malam Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana cewa yanzu haka hukumarsa ta samu nasarar kwato makudan kudade da kadarori na sama da Naira biliyan daya da rabi a cikin shekara guda kawai.
Malam Muhuyi ya bayyana hakane a lokacin wata ganawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a makon da ya gabata.
Ya kara da cewa yana godiya ga Allah a kan samun nasarar hukumar ta canza mata fasali wanda ya dace da zamani har jama’a suka fahimci hukumar da irin aikinta wanda hakan ne ya sa jama’a ke kai karar mutanen da suke zargin sun tauye musu hakki na kadarorinsu ko na kudadensu.
Ya ce a yanzu haka sama da mutane 2000 ne suka kai kara a wannan hukuma a cikin shekara guda, wanda kuma duk korafi da aka kai, hukumar ba ta bata lokaci ba wajen bincike da gano gaskiyar lamarin domin baiwa mai hakki hakkinsa.
Haka kuma ya ce hukumar na da jami’ai a kananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano wanda hakan ce ta ba da dama ga al’ummar yankunan karkara ta fahimtar ayyukan hukumar inda aka samu ninki ba ninki na rubanya karbar korafe korafe da ya fi na baya akalla sau uku kuma wannan nasara ce ga hukumar da daraktocinta da ma’aikatanta, da Gwamnatin Kano da sauran al’umma da suke aiki hannu da hannu ta hanyar shawarwari da fahimtar juna a jihar.
Haka zalika, ya ce hukumar na aiki da hukumomi da kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa domin tabbatar da adalci da kuma yakar zalinci a kowane mataki.
Domin a cewarsa, yaki da cin hanci abu ne mai cike da kalubale ta yadda mutum yana yaki da cin hanci da rashawa shi ma yana yakar sa, dan haka ya ce ba za su saurara ba a kokarinsu na tabbatar da da adalci da kuma yakar zalinci a kowane lokaci.
Comments