Dakarun Senegal sun kutsa Gambia
Dakarun Senegal sun shiga kasar Gambia domin tabbatar da cewa Adama Barrow ya karbi mulki a matsayin sabon shugaban kasar.
Hakan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da Mr Barrow ya sha rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin kasar da ke babban birnin Senegal.
Tuni kasashen duniya suka amince da shi. Amma Yahya Jammeh wanda ya dade yana kan mulki ya ki sauka kuma majalisar dokoki na mara masa baya.
Kasashen yammacin Afirka sunyi barazanar cire shi dakarfin tuwo. Majalisar Dinkin Duniya ma ta amince da Mista Barrow.
Kasashe mambobin kwamitin sulhu na majalisar sun goyi bayan amfani da karfi amma sun ce "matakin siyasa za a fara bi da farko".
Comments