Mutane biyu sun mutu lokacin wasan hawan kaho a India

Mutane biyu ne suka mutu, bayan da saniya ta soke su a lokacin wasan gargajiya na hawan kaho a jihar Tamil Nadu ta kasar India.
An dawo da wasannin gargajiyar na jallikattu da aka saba yi a lokacin girbi na watan Janairu ne, bayan da gwamnati ta shige gaba wajen ganin kotun kolin kasar ta dahe haramcin da ta yi wa wasannin.
Wasu jama'ar da suka taru sun sha kauracewa wasannin gargajiyar na jallikatu-- ba wai saboda batun azabtar da dabobin , da kuma hadarin da ke tattare da hakan bane, amma saboda suna son a sake halarta shi.
Sarrafa mafadatan shanun abu ne da aka dade ana yi a jihar ta Tamil Nadu, a matsayin wasannin gargajiya, da kuma wasu tsatsube-tsatsube lokacin girbi.
A shekarar 2014 ne kotun kolin India ta haramta wasan hawan hako, a karkashin dokar kasar hana azabtar da dabbobi.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya