Shugaba Buhari Na Nan A Raye Kuma Cikin Koshin Lafiya, Cewar Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu sakamakon jita-jitar da wasu kafafun yada labarai suka soma yadawa na cewa shugaban kasar ya rasu.
Idan ba a mance ba dai, a ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaba Buhari ya tafi hutun kwanaki goma kasar Ingila, inda zai yi amfani da wannan damar wajen duba lafiyarsa.
Comments