An Yi Adu’oin Tunawa Da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa

An gudanaqr da adu’oin da ya sami halartar mutane daga kowanne bangaren rayuwa na kasar, a gidan marigayin dake titin kofar rana cikin garin Bauchi,
Wazirin Bauchi Alhaji Waziri Kirba wani dattijo mai kimanin shekaru tamanin da haihuwa, yana daga cikin almajiran marigayi Tafawa Balewa. Ya bayyana cewa, marigayin shine malaminsu na tarihi da turanci bayan dawowarsa daga karatu Ingila. Ya bayyana marigayin a matsayin mai tausayi.
Babban dan marigayi Tafawa Balewa, Baba Abubakar ya bayyana mahaifinsa a matsayin wanda ya sadaukar da kanshi domin yiwa kasa hidima, ya kuma yi aiki domin ganin hadin kan Afrika baki daya da suka zama abin koyi.
Sauran wadanda suka yi jawabai a wajen addu’ar sun yi kira ga sauran al’umma musamman ‘yan arewacin kasar su kasance masu kishin kasa da sadaukar da kai domin yiwa kasa hidima da kuma ganin ci gaba da hadin kan kasa.
Wata kungiya dake hankoron ganin ci gaban Bauchi karkashin jagorancin Zahradeen Baban Tanko ce ta shirya zaman addu’oin.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya