Wasu shugabannin kasashen Afirka ta yamma, sun fara tattaunawa a Abuja babban birnin Nijeriya don warware rikicin siyasar kasar Gambia.

Daga cikin shugabannin da ke halarta taron,wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke jagoranta, har da Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia, da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama wanda ya mika mulki a shekaranjiya Asabar.
Shugaban Gambia, Yahya Jammeh dai ya ki amincewa da mika mulki bayan an kada shi a zabe cikin watan jiya.
Hukumomin kasar sun rufe gidan rediyo na 4 a jiya Lahadi, inda ma'aikatan Paradise FM suka ce 'yan sanda sun umarce su, su dakatar da yada shirye-shirye.
Ba su bayar da wani dalili kan daukar wannan mataki ba.

Comments

Popular posts from this blog

Hotuna: Kyautar Da Yan Shia Suka Ba CAN Yau A Bauchi

Hotuna: Garin Da Ya Fi Ko Wane Gari Sanyi A Duniya