An rantsar da Adama Barrow shugaban Gambia
Adama Barrow ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban ƙasar Gambia a ofishin jakadancin kasar da ke Senegal.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta Gambia Sheriff Tambadou ne ya rantsar da shi.
A yanzu kasar na da mutum biyu da ke ikirarin kasancewa shugabanninta.
Mista Barrow ya je Senegal ne bayan yunkurin da kungiyar Ecowas ta yi na ganin Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin ruwan-sanyi ya gagara.
A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh zai ƙare a kan mulki, ko da yake majalisar dokokin ƙasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.
Senegal ta bashi zuwa tsakar daren ranar Talata domin ya sauka, ko kuma ta afka masa.
Tuni dakarun kasar da na Najeriya da Ghana suka isa kan iyakar Gambia domin shirin kifar da Mista Jammeh da zarar sun samu izini.
Comments