Har Yanzu Tsugune Ba Ta Kare Ba Tsakanin Tsohon Gwamnan Kano Na Da, Da Na Yanzu

VOA Hausa

Bisa alamu har yanzu akwai rashin jituwa tsakanin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar na yanzu Dr Abdullahi Ganduje wanda lokacin Kwankwaso shi ne mataimakin gwamna.
Inji Gwamna Ganduje yace an samu rashin jituwa jim kadan bayan an mika mulki ga gwamnatinsa.
Misali, kawamitin mika mulki wanda shi ne ya jagoranta ya gano cewa akwai bashin biliyan dari ukku da ake bin jihar. Amma Gwamnan Kwankwaso bai ji dadin yadda aka fito da alkaluman ba.
A cewar Gwamna Ganduje Kwankwaso yace babu mai binsa ko kwabo har da cewa duk wanda aka ba aiki an gama biyansa to saidai tun bai mika mulki ba 'yan kwangila suka yi ca suka karyata ikirarinsa.
Gwamna Ganduje yace ya fada masa cewa batun bashi ba magana ba ce domin babu gwamnatin da za'a yi da ba'a binta bashi. Kuma barin bashi ba laifi ba ne.
A lokacin da farashin mai ya fadi shugaban kasa Muhammad Buhari ya ga cewa jihohi ba zasu iya biyan albashi ba sai an basu tallafi. Sai Sanata Kwankwaso ya ba Ganduje takarda a rubuce cewa shi bai yadda ya karbi tallafi daga gwamnatin tarayya ba. Yace sai 'yan majalisa sun amince kafin ya karbi tallafi daga gwamnatin tarayya.
Inji Gwamna Ganduje abun da Sanata Kwankwaso ya keso shi ne jihar ta kasa biyan albashi domin ya nunawa jama'a cewa a lokacinsa shi yana biyan albashi.
Baicin hakan akwai wadanda suka baibayes shi Sanata Kwankwaso kuma in banda zagin gwamnati babau abun da su keyi. Ganduje yace duk wani abu na alheri sai sun yi suka a kai.
Dangane da yin sulhu tsakaninsu, Gwamna Ganduje yace sun kafa kwamitoci domin kawo daidaituwa da hadin kan 'yan jam'iyyar APC a jihar domin a yi tafiya mai karfi tare.
Wata babbar takaddama tsakaninsu ita ce ta shugaban APC na kasa. Yayinda Sanata Kwankwaso ya hakikance akan tsohon shugaban jam'iyyar shi ko Ganduje bai yadda dashi ba, wani daban ya keso. Yace a duba tsarin jam'iyyar a san abun da yakamata a yi idan ana son tsige shugaban jam'iyya. Yace sun duba tsarin sun ga kuma sun bi gaskiya akan tsige shugaban kuma wanda yake kai yanzu shi zai cigaba da kasancewa har a yi wani zabe.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya