Rundunar sojin ECOWAS ta gano makamai a gidan Yahaya Jammeh
Dakarun sojin Yammacin Afirka da aka tura kasar Gambia ta ce ta gano makamai a gidan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jammeh.
Kungiyar ECOWAS ta ce an gano makamai da harsasai ne a gidan Yahya Jammeh dake cikin kauyen Kanilai.
Mista Jammeh ya bar kasar kwanaki 10 da suka wuce bayan da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da shugaba Adama Barrow ya yi nasara a watan Disambar bara.
Mista Barrow ya bukaci dakarun ECOWAS su zauna a kasar don tabbatar da kwanciyar hankali a lokacin da tsohon shugaban ya bar Gambia.
Comments