Hotuna: Dubban mata na gudanar da zanga-zanga a birnin Washington DC.

Kwana daya bayan rantsar da shugaban Amurka Donald Trump wanda ya sami halartar dubu dubatan mutane a birnin Washington, wata kungiyar mata tana gudanar da wani gagarumin gangami a majalisar dokokin Amurka da sauran wasu wurare a fadin Washington DC, domin nuna adawa da manufofin sabon shugaban kasar.
Kungiyar da ta hada gangamin matan mai taken Women’s March, sunce suna kyautata zaton dubban mutane zasu halarci gangamin yau asabar.
Jami’ai a birnin Washington sun ce motocin safa dubu daya da dari takwas ne suka yi rajista domin samun izinin ajiye motocinsu a Birnin Washington, wanda ke nufin cewa, kimanin mutane dubu dari zasu zo gangamin ta motocin safa kadai.
Ana kuma shirin yin irin wannan jerin gwanon a manyan birane ishirin na duniya da suka hada da birnin London da Berlin, da Nairobi da kuma Sydney.
Wadanda suka shirya gangamin na Washington sun ce suna son su aika sako ga Trump a wuninsa na farko a matsayin shugaban kasa cewa, ‘yancin mata, ‘yanci ne na bil’adama. Masu gangamin sunce zasu bukaci samun daidaito a fannin launin fata da jinsi, da kiwon lafiya, da ‘yancin zubar da ciki, batutuwa da suka ce suna fuskantar barazana karkashin shugabancin Tump.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya