Gwamnan Jihar Kano Ya Bayyana Dalilin Ciwo Bashin Dala Kusan Biliyan Biyu
VOA Hausa
Tun lokacin da gwamnatin jihar Kano ta sanar da ciwo bashi domin aiwatar da wasu ayyukan jin dadi da inganta tattalin arzikin jihar wasu suka shika sukarta lamarin da ya sa Muryar Amurka ta ji ta bakin gwamnan Dr Abdullahi Ganduje.
Yaynda da gwamnan yayi fira da Muryar Amurka ya soma da cewa jihar Kano ta fi kowace jiha yawan al'umma a duk fadin Najeriya kana birnin Kano shi ya fi kowane birni yawan jama'a a jihohin arewa.
Idan aka kula akwai maganar sufuri da zirga-zirga kuma duk inda aka samu yawan jama'a dole ne a saukaka hanyar zirga zirga, inji gwamna Ganduje.
A cewar Dr Ganduje birnin Fatakwal na jihar Rivers ana nan ana gina layin dogo domin inganta harkaokin sufuri da bashin bankuna. Haka ma Legas tana gina layin da kudin banki. A birnin Kaduna ma zasu fara gina nasu wannan watan.
Inji Dr Ganduje duk wanda ya san girman Kano yace bata bukatar jirgi bai san abun da zamani ke ciki ba ne.
Aikin na Kano wai an kasashi kashi hudu kuma duka za'a yisu akan kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari takwas kuma za'a gina wajen kilomita tamanin na layin dogo da kuma jiragen da za'a dora kansu.
Gwamnatin jihar zata dauki rukunin farko wanda zai ci dalar Amurka miliyan dari biyar da hamsin da biyar. Amma banki zai bada kashi tamanin da biyar cikin dari, gwamnati kuma zata bada goma sha biyar cikin dari.
Bayan an kammala aikin kudin da mutane zasu dinga biya na shiga jirgin dashi za'a rika biyan bankunan. Za'a dauki wajen shekaru goma sha biyar ana biya a hankali. Bayan an gama biya komi kuma ya zama mallakar jihar da kananan hukumominta. Kasar China ce zata yi aikin.
Comments