Gobara ta kona shaguna fiye da 50 a Potiskum
Wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Potiskum da ke jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta kona akalla shaguna 50 na jama’a.
Gobarar wadda ta shi da misalin karfe 1 na daren daya gabata, ta fi yin illa a bangaren masu hada-hadar kayan gwanjo da teloli da kuma bangaren da ake siyar da kwanuka.
Comments