Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Shehu Shema A Kotu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a gaban wata babbar kotun jiha bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Ana dai zargin tsohon gwamnan ne da wasu mutane uku da karkatar da Naira biliyan 11 na kananan hukumomi a lokacin mulkinsa daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A zaman kotun da aka yi yau Talata a birnin Katsina, lauyoyin tsohon gwamnan sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar, yayin da su kuma lauyoyin EFCC suka kalubalanci lauyoyin masu kare wanda ake tuhuma.
Babbar kotun dai mai lamba 3 ta sanya ranar 7 ga watan gobe domin bangarorin biyu su tafka mahawara kan batun hurumin kotun.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya