An cafke masu safarar fatar Jaki a Afurka ta Kudu
'Yan sandan kasar Afurka ta Kudu, sun ce su na gudanar da bincike kan safarar fatar Jaki ba bisa ka'ida ba, inda suka kwace sama da fatu 5000 a wani wuri da ake boye su, lokacin da suka kai samame gabashin birnin Johannesburg.
'Yan sandan sun yi zargin fatun jakin da suka kama a gidan gona da ke garin Benoni a makon da ya wuce, an same su ne bayan 'yanka dabobi ba bisa ka'ida ba da ake kaiwa kasar China.
An kai wannan samame ne, bayan wata mace ta yi korafin ta na jin warin rubabben nama a kusa da gidanta.
Babu dai wanda 'yan sandan suka cafke ya yin samamen, sai dai kuma sun yi nasarar gano yadda ake yanka dabbobi ba bisa ka'ida ba a boyayyen yankin.
Ana samun miliyoyin daloli a kasuwancin fatar Jaki dai, inda suka fi yin tsada a kasar China saboda ana amfani da ita wajen yin magani.
Magungunan da ake samarwa da fatar jaki sun hada da, maganin daidaituwar jinin al'ada ga mata, da tsawaita shekarun jinin al'ada da sauransu.
Comments