Mutuwar Baba Masaba, ta sanya mata 113 takaba.

Baba Masaba, wanda asali mutumin garin Bidda ne da ke jihar Niger a Arewacin Najeriya, ya mutu ranar Asabar.
Rahotanni sun ce ya mutu ne yana da shekara 93, inda ya bar 'ya'ya kimanin 137.
Baba Masaba dai ya yi fice ne saboda yawan mata da 'ya'yansa.
Shi dai marigayin - wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya - ya fito fili ne bayan da a wata hira ta musamman da ya yi da BBC ya ce ya auri mata 86 kuma dukkansu suna tare da shi a lokacin, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce tsakaninsa da Malaman addinin Musulunci na kasar.
Bayanai sun nuna cewa Baba Masaba yana biya wa duk iyalinsa bukatunsu na rayuwa duk kuwa da yawansu.
A wani lokaci can baya ma jami'an tsaro sun taba tsare shi a birnin Minna na jihar, saboda auren mata rututu, abin da ya saba wa addinsa na Musulunci.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya