In har kana tsammanin tsananin sanyin da ka ke ji, ko ka taba ji, a garinku ko a wani wuri ya kai tsanani, to ka sake tunani. Barka da zuwa Oymyakon, garin da ke arewacin Rasha, kuma garin da aka yi ittifakin ya fi ko wanne gari sanyi a duniya. Tsanin sanyin Oymyakon, ya kai −71.2 °C a ma'aunin da aka auna a shekarar 1924. A wannan watan na janairu, dumi da ka iya samu shi ne -50°C (-60°F). Fitaccen mai daukar hoton nan na New Zealand, Amos Chapple, ya kai ziyara garin na Oymyakon.
Alhaji Shamsudeen Dalhatu Zango babban masoyin shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya tashi tun daga Nijeriya har zuwa birnin London dake kasar Ingla kawai saboda idanunsa su gane masa gidan da shugaba Muhammadu Buhari ke zaune a ciki. Shi fa ba wai sai ya ga Shugaba Muhammadu Buhari ba, a'a kawai burinsa ya yi ido hudu da katangar gidan da baba yake ciki. Burinsa ya cika gashi nan a kofar gidan da Baba yake a birnin London.
Comments