Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sake Mika Sunayen Sabbin Jakadu Amma Ba Tare Da Sunayen Sanata Olorunimbe Mamora, Dr Usman Bugaje Da Pauline Tallen Ba
Shugaba Muhammadu Buhari ya sake mika sunayen sabbin jakadu amma ba tare da sunayen sanata Olorunimbe Mamora, Dr Usman Bugaje da Pauline Tallen ba, wadanda ke cikin jerin da aka mika a bara.
Majalisar dattawa dai a bara ta yi watsi da jerin sunayen da shugaba Buhari ya tura mata, sakamakon cece-kucen da ya biyo baya.
Amma a yau, alhamis, shugaban majalisar Bukola Saraki ya karanta wasikar shugaba Buhari a majalisar. Kuma cikin karin da aka samu har da Ibrahim Ugbada.
Comments