Abin da ya sa ba zan kori Babachir ba — Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ba zai kori sakataren gwamnatin kasar ba kamar yadda majalisar dattawan kasar ta bukata saboda bai gamsu da hujjojin da suka bayar ba.
Shugaba Buhari ya ce ba duka 'yan kwamitin da suka binciki Babachir Lawan ne suka sa hannu kan rahoton kwamitin ba.
A wata wasikar da shugaban ya aika majalisar wadda shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya karanta, ya ce shi bai yi aiki da shawarwarin rahoton ba, saboda mutum uku daga cikin mambobin kwamitin ne suka saka hannu, yayin da mutum tara basu saka hannu ba.
Wasikar ta kara da cewar kwamitin bai bai wa Babachir Lawan damar kare kansa ba, kuma kamfanin da ake zargin na Babachir ne shi ma bai samu damar kare kansa ba.
Comments