‘Yan mata biyu sun kai harin kunar bakin wake a Kaleri
Wasu mata biyu sun kai harin kunar bakin wake a Kaleri da ke cikin karamar hukumar Mafa a Jihar Borno inda suka halaka Kansu kuma suka kashe mutane biyu.
‘Yan matan sun kai harin ne a cikin dare misalin karfe 10:30, kamar yadda wakilin RFI Hausa Bilyaminu Yusuf ya tabbatar.
Bilyaminu ya ce yanzu ‘Yan ta’addan sun bullo da wani sabon salon kai hari inda suke kwankwasa kofar gidajen mutane idan an bude su tayar da bom din da ke jikinsu.
A karshen watan Disemba ne sojojin Najeriya suka sanar da nasarar murkushe ‘Yan Boko Haram a Dajin Sambisa, amma har yanzu mayakan na ci gaba da zama barazana inda suke kai hare haren sari-ka-noke a kauyukan Borno a Najeriya da kuma makwabta a Nijar da Chadi.
ha.rfi.fr/afrika/20170109-yan-mata-biyu-sun-kai-harin-kunar-bakin-wake-kaleri
Comments