Tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hashemi Rafsanjani ya rasu.
Ya rasu ne yana da shekaru tamanin da biyu a duniya.
Marigayi Ali Akbar Hashemi Rafsanjani, mai fada a ji ne a siyasar kasar tun a shekarun 1980.
A ranar Lahadin nan ne aka kai shi asibiti sakamakon ciwon zuciya.
Shi ne shugaban Iran daga shekarar 1989 zuwa 1997, amma da ya sake neman shugabancin kasar a 2005, bai yi nasara ba, inda aka zabi Mahmoud Ahmadinejad.
Comments