Me ya sa sana'ar saka ke neman 'gushewa'? Usman Minjibir BBC Hausa

Garin 'Yan zaki na karamar hukumar Minjibir a jihar Kano, na daya daga cikin garuruwa da dama a arewacin Najeriya da suka shahara a wannan sana'a.
Sai dai kuma masaƙan garin wadanda mafiya yawansu dattijai ne sun koka cewa zai yi wuya sana'ar ta dore bayan ransu.
Malam Danladi Gambo, mai shekara fiye da 60, ya kwashe fiye da shekara 55 yana sana'ar saƙa.
Amma ya ce da alama sana'ar ba za ta yi nisan kirki ba daga kansu saboda zamani da kuma rashin samun riba a sana'ar.
"Ka ga masaƙa a nan wurin ta fi guda 20 amma duba ka ga sauran nawa yanzu. Mutum shida sun mutu a nan wurin amma ba su sami magada ba."
Ɗanlarai 'Yan Zaki, shi ma wani masakin ne da ya gaji sana'ar kuma ya kwashe fiye da shekara 50 yana yin wannan sana'a.
Uma kamar sauran masaka, malam Ɗanlarai yana bayyana fargabar rashin samun magaji.
"Na gaji wannan sana'a daga wurin mahaifina kuma shi ma ya gada daga mahaifinsa. To amma kash! ba na jin za a samu wanda zai gaje ni saboda rashin gudanawar sana'ar."
Fargabar da wadannan tsaffi ke da ita na neman tabbata bisa la'akari da abin da wani yaro wanda ya ci kwalliya kuma yake kallon masakan ya shaida min.
Yaron mai suna Abdullahi dai ya ce ba ya fatan zama masaki saboda babu kudi a harkar.
"Direba nake son zama ba masaƙi ba domin babu kudi a sana'ar saka," in ji shi.
Shi ma Nuhu Idris wanda matashi ne ya shaida min cewa rashin samun kudi ne ya sanya shi gujewa sana'ar ta saka zuwa aikin koyarwa.
"Ya kamata ace muna yin wannan sana'a ta saka tun da gado ce amma saboda wahalar da ke ciki shi ya sa muka yi watsi da ita."
To sai dai har yanzu za a iya cewa ba a rasa yara daya zuwa biyu masu sha'awar yin sana'ar da suka gada iyaye da kakanni ba, kamar Sani Tukur.
Sani, dan shekara 13, yana ta faman kai gwauro ya kai mari, a inda yake murza zare da kwarkwaro a cikinsa.
Ya shaida min cewa "Mahaifina ba shi da lafiya yana kwance a gida saboda haka ni ina wannan sana'ar ne domin na gaje shi."
Masakar garin na 'Yan Zaki dai ta shahara wajen saƙar rigunan saƙi da zannuwa da rawani da huluna da ma likkafani.
To amma kawo yanzu masu sana'ar sun ce saƙa ta zama sana'ar yin likkafani kawai domin shi ne ya fi samun kasuwa.
Sai dai kuma masakan sun ci alwashin janyo hankalin 'ya'ya da jikoki domin su yi sha'awar sana'ar amma bisa sharadin idan da za su sami tallafi.
Yanzu dai za a iya cewa masakar 'Yanv Zaki ta zama wani wuri da 'yan yawon bude ke zuwa su dauki hoto kawai.
Da kuma mutanen za su sami tallafin da suke bukata, watakila da fargabar Malam Gambo ta gushewar sana'ar, ta kau.

Comments

Popular posts from this blog

Hotuna: Kyautar Da Yan Shia Suka Ba CAN Yau A Bauchi

Ya Tashi Tun Daga Nijeriya Har Zuwa London Saboda Ganin gidan Da Shugaba Muhammadu Buhari Ke Zaune A Ciki