Ana bin Najeriya bashin Naira Tiriliyan 17
Gwamnatin Najeriya ta ce yanzu haka bashin da ake bin ta ya kai sama da Naira tiriliyan 17 wanda ya kunshi har da na jihohi daga sassa daban daban. Shugaban hukumar da ke kula da basusukan gwamnati, Abraham Nwankwo ne ya bayyana kididigar a gaban kwamitin Majalisar Dattawa.
Nwankwo ya ce adadin bashin na triliyan 17 ya kunshi bashin da gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 da Abuja suka ciyo daga cikin gida da kuma na kasashen waje.
Jami’in ya ce daga cikin wannan adadi, kashi 80 na basusukan Jihohi ne suka ciwo su.
Gwamnatin Buhari dai ta nemi kara ciyo bashi domin cike gibin kasafin kudin 2016.
Najeriya dai na fama da matsalar tattalin arziki saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya wanda kuma ya janyo faduwar darajar Naira.
Comments