Dan Shekara 28 Ya Auri Tsohuwa Yar Shekara 82
Kwanan baya ne wani matashi mai aikin kwadago Sofian Laho Dandel ya shiga soyayya da wata tsohuwa Martha mai shekaru fiye da 80 a Indonesia.
Kamar yadda jaridar Tribune News ta ruwaito, yanzu har an shirya aure duk da bambancin shekarun na su. Martha dai tsohuwa ce wadda ta rasa mijinta shekaru fiye da 10 da suka wuce, ta kuma ce yanzu ita da Sofian, mutu ka raba; takalmin kaza.
Comments