Jam’iyyar PDP za ta yi maja da jamiyyu bakwai kafin zaben 2017 – Inji Jerry Gana

Jam’iyyar PDP ta ce za ta yi maja da wadansu jam’iyyu bakwai kafin tunkaran zaben 2017.
Tsohon ministan watsa labarai Jerry Gana ne ya sanar da hakan ne da yake mika rahoton kwamitinsa da uwar jam’iyyar ta nafa domin bata shawarwari akan hanyoyin da za ta bi domin warware matsalolin da ta ke fama da su yanzu.
Jery Gana yace jam’iyyar na tattaunawa da wadansu jam’iyyu a kasa Najeriya domin yin maja kafin zaben 2019.
Tsohon ministan ya ce yana da tabbacin cewa jam’iyar APC ba za ta kai labari ba a zaben 2019 musamman ganin irin shirin da jam’iyyarsa ta ke yi domin tunkarar 2019.
Ya kuma karyata jita jitan da ake ta yada wa wai jam’iyar PDP za ta canza suna bayan tayi maja da wadansu jam’iyyu .
Jerry Gana yace jam’iyyar PDP ba za ta canza sunanta ba.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya