RAHOTO: Ganduje Na Aiki, Sai Dai Rashin Bayani A Jaridu — Sanata Rufai Sani Hanga

Tsohon Sanata a Mazabar Kano ta Tsakiya, Alhaji Rufa`I Sani Hanga ya bayyana cewa Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tana aiki sosai ta kowane fanni sai dai kawai rashin wayar da kan Jama`a akan aiyukan da ta ke yi a jaridun kasar nan da sauran kafafen yada labarai.
Ya ce wannan shi ne kawai abin da Gwamnatin Kano ta rasa wanda kuma ba karamar koma baya ba ne a tafiyar da harkar gwamnatin dimokuradiyya.
Sanatan ya bayyana hakan ne lokacin da wata tawagar matasa da ta ziyarce shi a gidan sa a makon da ya gabata.
Ya kara da cewa zuwan Gwamna Ganduje ya kirkiro sababbin aiyuka na bunkasa ilimi da lafiya da sauran fannoni na cigaban Al’ummar Jihar Kano wanda a baya ba a yi ba.
“Ya zo ya dora aikin da ya gada na tsohon Gwamna Kwankwaso kamar gadoji da titina a Jihar Kano, haka kuma ga aikin da ya dora a kan ayukan tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau na ginin da ya soma na Asibitin Unguwar Giginyo cikin Birnin Kano, ga kuma aikin ginin Katafaran Asibitin Yara mafi girma a Afrika a kan Titin gidan Zoo wanda wadannan aiyuka, Malam Ibrahim Shekarau ne ya fara bai kammala ba, da Kwankwaso ya zo bai kammala ba, amma shi Ganduje saboda kishin sa har ya kammala saura kadan a fara aiki a asibitocin biyu”.
Haka zalika Hanga ya ce duk inda ka za ga a Jihar Kano za ka inda ya ke aikin Tituna a ko ina ga kuma biyan albashin ma`aikata a kan lokaci duk da irin matsalolin da suka shafi tattali arzikin kasar nan, “wannnan ba ta hana Ganduje aiki ba, yana ta yi ba ji ba gani domin bunkasa Kano da Kanawa” a cewar Sanata Hanga.
Ya ci gaba da cewa, “Haka kuma in ka dawo bangaren gidaje wanda talaka zai iya siya sabanin abun da aka yi a baya suna nan sun zama marasa amfani amma wadannan kuwa ana yin su ne don talaka ya amfana”. In ji shi
Danga ne da Siysar kasa kuwa, Sanata Hanga ya ce wajibi ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemo wadanda za su taya shi aiki da suka wadanda suke kewaye da shi kishin kasa.
“Shugaban Kasa Muhammadu ya gagaguta yiwa ministocinsa ritaya, sannan ya zo da wani tsari da talakan kasar nan zai samu sassauci na tsadar rayuwa domin rufe kan iya ka da hana shigo da abinci ya jefa talaka cikin wani kunci na rayuwa.
Sanatan ya ce duk da wannan matsi da ‘yan kasa ke ciki, ya ce Gwmnatin Buhari ta samar da cigaba ta fannin tsaro da nasara wajen dawo da zaman lafiya.
“Wannan nasara da aka samu ta fito da Matsalar PDP karara wanda a zamanin ta Jama`a suka dandana kudar su wanda ya sa jama`a ba za su sake zabar Jam`iyyar PDP ba a kasar nan ba har abada,” a cewarsa.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya