Posts

Hotuna: Fayose Da Makarfi A Wajen Taron Masu Ruwa Da Tsaki Na PDP

Image
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sen. Ahmed Makarfi tare da shugaban majalisar gwamnonin PDP, Ayodele Fayose a wajen taro.

Fadar Shugaban Kasa Ta Wanke Sakataren Gwamntin Tarayya daga Zargin Yin Almundahana

Image
Wanda yake cikin kwamitin da ya binciki kwangilar yanke ciyawa ta miliyoyin Nera yace sun yi aiki kainda nain kuma wasikar shugaban kasa da ta wanke Lawal Babachir yunkuri ne na neman a birkitar da gaskiya. Shugaban kwamitin 'yan gudun hijira na majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya maida martani ga wasikar da ta fito daga ofishin Shugaba Buhari dake nuna cewa ba'a yiwa sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal adalci ba kan batun nome ciyawar kachalla. Wasikar da shugaban majalisar dattawan ya karanta tace mutane ukku kachal ne cikin tara suka sanya hannu cikin rahoton binciken da ake zargin sakataren gwamnati da yin zarmiya. Kazalika ba'a gayyaci shi sakataren ba ko 'yan kwangilar domin su kare kansu lamarin da ya sa shugaba Buhari ya ki amincewa da bukatar cire David Lawal Babachir daga mukaminsa. Amma Shehu Sani yace yanada takardar gayyatar sakataren gwamnatin haka kuma wai mutane bakwai ne cikin tara suka sanya hannu akan rahoton. Saboda haka zasu cigaba da f...

Hotuna: Yan Sanda Sun Tarwatsa Yan Shia A Harabar Majalisar Wakilai Ta Tarayya

Image
Dandazon 'yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da 'yan Shi'a sun fara zanga-zangar neman a saki shugabansu El zakzaky,  a harabar majalisar wakilai ta yarayya. A lokacin ne 'yan sanda suka fara buga musu barkonon tsohuwa, daga nan ne kuma kowa ya cika rigarsa da iska.

Sabon Shugaban Kasar Gambiya Zai Koma Gida Gobe

Image
Dan jarida Sainey MK Marenah ya tabbatar da cewa shugaban kasar zai koma Gambiya gobe 26 January 2017, daga Dakar, Senegal.

Mace daya cikin 10 na jin zafi lokacin jimai

Image
Wani bincike da masana kimiyya suka yi ya nuna cewa kusan kowacce mace daya cikin mata 10 na matukar shan wahala a lokacin da ake yin jima'i da su. Binciken da aka yi kan kusan mata 7,000 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 74, wanda aka wallafa a mujallar Birtaniya mai suna British Journal of Obstetrics and Gynaecology , ya ce wannan matsala, wacce a kimiyyance aka sanya wa suna dyspareunia - ta zama gama-gari kuma tana shafar mata manya da kanana. Sai dai binciken ya nuna cewa lamarin ya fi faruwa ga matan da suka haura shekara hamsin da doriya zuwa sittin da kuma 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 24. Amma likitoci sun ce ana iya magance matsalar. Ana alakanta jin zafi lokaci jima'i da wasu matsalolin da suka danganci jima'i kamar bushewar farji da fargaba lokacin jima'i da kuma rashin jin dadin jima'in. Wasu matan sun ce suna tsoron yin jima'i ne saboda suna matukar jin zafi.

Trump Na Gab Da Hana Baki Shiga Amurka

Image
A wannan larabar ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai sanya hannu kan dokokin takaita shigar baki kasar kamar yadda ya bayyana lokacin yakin neman zabensa. Rahotanni sun ce dokokin za su takaita bai wa bakin da suka fito daga kasashen Iraqi da Iran da Libya da Somalia izinin shiga Amurka. Sauran kasashen da dokar zata shafa sun hada da Sudan da Syria da Yemen A sakon da Trump ya aika ta kafar twitter ya ce lallai za su gina katangar da ya yi alkawari tsakanin Amurka da Mexico. Kasa da mako guda da kama aiki, Mista Trump, ya aiwatar da muradai da dama sune jigo a yakin neman zaben da ya kayar da Hillary Clinton. Shugaba Trump ya ce aikinsa shi ne kare Amurka da muradunsu.

Direbobin Manyan Motoci daga Arewa Sun Daina Ba Jami'an Tsaro Na Goro

Image
Gamayyar kungiyoyi da suka hada da masu sarrafa kayan gona, direbobin manyanmotoci da fataken shanu dake safara daga arewa maso gabas zuwa kudancin Najeriya sun tsaida shawarar daina baiwa jami’an tsaro abin goro a shingayen manyan hanyoyi biyo bayan taronsu kan abinda suka bayyana musgunawa da takura masu da a keyi. Mai Magana da yawun gamayyar kungiyoyin shugaban masana’antar sarrafa anfanin gona na Dak Farm And Milling Industry da ke Jos fadar jihar Filato Sir Mohammed Ali ya ce daga cikin kudurorin da suka dauka akwai na ladabtar da duk wani direba da ya baiwa jami’ai cin hanci a shingayen manyan hanyoyi. Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta fito da tsari na bai daya wanda za a amince da shi a duk sassan kasar don maye gurbin tarin kudaden da suke biya wadanda hukumomi da ke kafa irin wadannan shingayen basu mutuntawa don rage musgunawa da suke fuskanta inj sarkin tashar Mubi dake jihar Adamawa Alhaji Usman Mai Nagge. Ya ce suna biyan kimanin naira dubu ashirin zuw...