Posts

EFCC ta kama tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu

Image
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC), ta kama tsohon gwamnan jihar Neja Dr Mu'azu Babangida Aliyu kan zargin cin hanci da rashawa da halatta kudaden haram. Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa da BBC cewa hukumar tana rike da tsohon gwamnan. "Yana hannunmu kuma muna cigaba da yi masa tambayoyi," in ji mista Uwujaren. Sai dai bai yi karin haske kan abin da ake tuhumur tsohon gwamnan da aikata wa ba. Hakazalika bai bayyana lokacin da hukumar za ta gurfanar da Dr Aliyu a gaban kotu ba. Tsohon gwamnan na Neja ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015. Kuma ya fadi takarar kujerar majalisar dattawa da ya nema a zaben 2015.

Yan Nigeria sun cika mita — Bincike

Image
Wani bincike a baya-bayan nan,na cewa 'yan Nigeria na sahun gaba a tsakanin al'ummomin kasashen duniya da suka fi mita da korafi kan shugabanninsu. Binciken wanda wata ƙungiyar bin diddigin mulkin dimokraɗiyya a duniya mai suna Good Governance Group ta fitar ya nanata buƙatar 'yan Nijeriya su sauya hali kan yadda suke kallon masu madafun iko da ma yadda gwamnati ke biyan buƙatunsu. Wani masani kan Dr. Abdullahi Yelwa masanin kan zamantakewa da halayyar ɗan'adam ya ce 'yan Nijeriya suna kallon shugabanninsu a kowanne mataki mutane masu ci-da-guminsu da ke fake da sunan wakiltar al'umma suna azurta kansu da iyalansu. Ana ganin rashin fahimtar gwamnati da kuma kaifin talauci sun taimaka wajen dusashe damar da 'yan ƙasar ke da ita ta ƙalubalantar shugabanninsu. Haka zalika, matsalar ta janyo ƙaruwar tumasanci da barace-barace Wani tsohon kantoman ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe, Alhaji Yusuf Yunusa ya ce jama'a ba sa tunkarar shugabanni d...

Sunayen sababbin kwamishinonin hukumar zabe da Buhari ya aika majalisa

Image
Yau ne majalisar dattijai ta karanta sunayen mutane 27 da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika majalisar domin amincewa da su kwamishinonin zabe. Ga sunayen: 1. Godswill Obioma, Abia 2. Ibrahim Abdullahi, Adamawa 3. Ahmed Makama, Bauchi 4. James Apam, Benue 5. Mike Igibi, Delta 6. Nwachukwu Orji, Ebonyi 7. Iloh Chuks, Enugu 8. Hussaini Pai, FCT 9. Sadiq Musa, Kaduna 10. Jibrin Zarewa, Kano 11. Asmau Maikudi, Katsina 12. Mahmuda Isah Kebbi 13. Samuel Egwu, Kogi 14. Rufus Akeju, Lagos 15. Mustapha Zubairu, Niger 16. Agboke Olaleke, Ogun 17. Sam Olumekun, Ondo 18. Abdulganiyu Raji, Oyo 19. Riskuwa Shehu, Sokoto 20. Kasim Geidam, Yobe 21. Bello Mahmud, Zamfara 22. Nentawe Yilwada, Plateau 23. Umar Ibrahim, Taraba 24. Emeka Joseph, Imo 25. Obo Effanga, Cross River 26. Francis Ezeonu, Anambra da 27. Briyai Frankland, Bayelsa

Wata mata ta watsa wa mijinta ruwan zafi a mazakutarsa

Image
Wata mata mai suna Kafayat ta watsa wa mijin ta ruwan zafi a mazakutarsa a garin Ibadan. Mijin nata wanda malamin makaranta ne mai suna Adelakun ya maka matar tasa a Kotu ya na neman a warware auren nasu. Ya fadi wa kotu cewa har yanzu ba zai iya amfani da mazakutarsa ba saboda konewa da tayi. Ko da yake Kafayat tace tsautsayi ne ya sa hakan ya faru dai dai tana rike da ruwan zafi amma ba wai tayi da gangar bane. Mijin nata dai ya umurci kotun da ta raba auren nasu domin ba zai iya zama da wannan mata ba.

Wanne hadari shan Fanta da Sprite ke da shi a Nigeria?

Image
Wata sharia'a da aka yi a baya-bayan nan a wata kotun Najeriya, ta bayyana cewa akwai yiwuwar lemukan kwalaba da ake yi a kasar na da hadari ga mutane, kamar yadda Ijeoma Nduke ta bayyana a rahoton da ta hada. Ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan da aka gano cewa wata kotu ta bai wa kamfanin da ke yin Fanta da Sprite na Nigeria bottling Company NBC, umarnin ya rika manna takardar da ke dauke da gargadi a kan lemukan da yake yi. Kotun ta bukaci kamfanin ya yi wa mutane gargadi cewa shan lemun tare da kwayar maganin bitamin C na da hadari kwarai. Masu suka na cewa lemukan na dauke da sinadarin benzoic acid da ya wuce kima da kuma kalar da ake sakawa. Sai kamfanin hada lemukan na NBC yana kalubalantar hukuncin. Lamarin ya jawo damuwa sosai a Najeriya, inda mutanen kasar da dama ke shan wadannan lemuka. Barbara Ukpabi, wata mai gidan sayar da abinci ce kuma tana sayar da abincin gargajiya iri-iri a unguwar Oniru da ke jihar Legas. Barbara ta ce akwai yiwuwar zata bar sayen Fanta ...

An samu naira miliyan 49 jibge a filin jirgin sama na Kaduna

Image
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) ta ce ta samu naira miliayan 49 a jibge a filin jirgin sama na Kaduna da ke arewacin kasar. Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce jami'anta sun kama kudaden cikin manyan buhuna biyar. Sanarwar ta ce an gane kudaden ne a lokacin da ake bincika kayayyakin matafiya kuma aka ga buhunan a jibge ba tare da mai su ba. Da aka bincika buhunan sai aka ga sabbin takardun kudi 'yan dari bibbiyu da kuma hamsin-hamsin. Sanarwar ta ce an fara bincike gadan-gadan domin gano masu safarar kudin. Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewar an samu kudaden yau Talata, inda ya ce an fara bincike domin gano wadanda suka kai kudaden filin jirgin saman na Kaduna. Ya kara da cewar kudaden ba na jabu bane. Amman bai ce ko waye hukumar take zargi da aikata laifin safarar kudin ba.

Dillalan Motoci Dokarmu Za Ta Shafa — Kwastam

Image
Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Najeriya wato Kwastam, ta ce ba a fahimci dokar da take son aiwatarwa ba dangane da batun karbar harajin shiga da mota kasar. Hukumar ta ce dokar ba ta nufin bincikar duk wanda ke da mota a kasar domin ganin ko ya biya kudin fito ko bai biya ba. Mataimakin shugaban hukumar ta Kwastam, Aminu Abubakar Dan Galadima, ya ce "Dokar za ta yi aiki ne kawai kan dillalan motocin da suka shigo da sabbin motoci cikin kasar ba tare da sun biya kudin fiton ba." Ya kuma ce babu haraji kan motocin da suka wuce shekaru takwas da kirkira. Sai dai kuma hukumar ta ce har yanzu tana kan bakarta ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasa. Ga dai yadda hirar ta kasance tsakanin Abdou Halilu na BBC da Aminu Abubakar Dan Galadima: Hukumar dai ta bayar da wa'adin wata guda domin fara aiwatar da wannan doka, al'amarin da ya sanya Majalisar Dattawan kasar ta yi wa shugaban hukumar kiranye. A ranar Litinin kuma shugaban hukumar, Hameed Ali, ya bayyana a gaban ...