Dillalan Motoci Dokarmu Za Ta Shafa — Kwastam

Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Najeriya wato Kwastam, ta ce ba a fahimci dokar da take son aiwatarwa ba dangane da batun karbar harajin shiga da mota kasar.
Hukumar ta ce dokar ba ta nufin bincikar duk wanda ke da mota a kasar domin ganin ko ya biya kudin fito ko bai biya ba.
Mataimakin shugaban hukumar ta Kwastam, Aminu Abubakar Dan Galadima, ya ce "Dokar za ta yi aiki ne kawai kan dillalan motocin da suka shigo da sabbin motoci cikin kasar ba tare da sun biya kudin fiton ba."
Ya kuma ce babu haraji kan motocin da suka wuce shekaru takwas da kirkira.
Sai dai kuma hukumar ta ce har yanzu tana kan bakarta ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasa.
Ga dai yadda hirar ta kasance tsakanin Abdou Halilu na BBC da Aminu Abubakar Dan Galadima:
Hukumar dai ta bayar da wa'adin wata guda domin fara aiwatar da wannan doka, al'amarin da ya sanya Majalisar Dattawan kasar ta yi wa shugaban hukumar kiranye.
A ranar Litinin kuma shugaban hukumar, Hameed Ali, ya bayyana a gaban kwamitin.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya