An Saki Mawakin Nan Na Kano, Sadiq Zazzabi

An gurfanar da Zazzabi a kan ya saki wata waka akan tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso, ba tare da bin ka’idar cibiyar sakin wakoki da bidiyo ba.
A yau Litinin, an bashi belin akan sharudda 3: Kudi N100,000, wani mamban kungiyar marubutan wakan jihar Kano, da kuma wani ma’aikacin gwamnati wanda ya kai akalla matsayi na 14.
Ya cika sharuddan belin kuma an sake shi kuma an dakatar da karar zuwa ranan 27 ga watan Maris. Zazzabi yace an tsare shi ne saboda cewa shi masoyin tsohon gwamna Kwankwaso ne.
Yayinda yake Magana da jaridar Premium Times, shugaban hukumar, Ismaila Afakallahu, ya tabbatar da cewa an sake shi.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya