MABIYA SHI,A ZA SU GURFANAR DA GWAMNA GANDUJE A KOTU
Jagoran Mabiya Shi'a a Kano Dakta Sanusi Abdulkadir Koki ya bayyana cewa sun kammala shirin su na gurfanar da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya bisa zarginsa da hada kai da hukumar 'Yan sanda aka kai musu hari a yayin tafiyarsu garin Zariya kimanin kwanaki dari da suka gabata.
'Yan shi'an sun bayyana cewa kimanin mutane 27 aka kashe musu tare da cafke 54 ciki hada mata da kananan yara.
Dr. Sanusi Abdulkadir Koki ya kuma kara da cewa a yayin gabatar da karar za su hada da kwamishinan 'Yan sanda wanda da shi aka yi amfani wajan cin zalinsu ba tare hakkinsu ba. Haka kuma ya tabbatar da cewa za su shigar da wata karar a kotun Duniya Ta I.C.C da nufin bin kadin hukuncin da Kotu ta yanke ga shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky kan a sake shi, tare kuma da biyansa diyya. Amma kuma gwamnatin tarayya ta ki bin umarnin kotu kamar yadda ya bayyana.
Daga karshe ya shedawa manema labaran cewa a yanzu suna yin addu'a tukuru kan Allah ya bi musu hakkinsu.
Comments