Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai taba iya takara da shugaba Muhamadu Buhari ba.
An samu rahotanni kwanakin nan daga jaridar Thisday cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na shirin takarar shugaban kasa a 2019 kuma ya fara neman shawarwari.
Tinubu wanda ya mayar da martini akan wannan lamar ta bakin mai magana da yawunsa, ya ce ba zai goyi bayan duk wanda zai yi takara da shugaba Buhari ba. Kuma ya jadadda goyon bayansa ga APC.
Comments