Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran manyan baki sun halarci bikin nadin Farfesa James Ayatse a matsayin Tor Tiv na 5

Nadin Tor Tiv din dai na zuwa ne bayan rasuwar margayi Tor Tiv na Hudu, mai martaba Alfred Akawe Torkula.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom shine ya jagoranci mika sandar girma ga sabon basaraken domin kama aiki.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin nadin sarautar sun hada da sarakunan gargajiya da Kakakin majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Rt Hon Yakubu Dogara, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar,
A wata sanarwa da Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai ya fitar yace akwai kuma wakilan Gwamnonin Zamfara, Borno, Sokoto, Kebbi, Kogi, Jigawa, Plateau, Taraba da Kwara da kuma ministoci da yan majalisu da dai sauran manyan baki.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya