An samu naira miliyan 49 jibge a filin jirgin sama na Kaduna
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) ta ce ta samu naira miliayan 49 a jibge a filin jirgin sama na Kaduna da ke arewacin kasar.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce jami'anta sun kama kudaden cikin manyan buhuna biyar.
Sanarwar ta ce an gane kudaden ne a lokacin da ake bincika kayayyakin matafiya kuma aka ga buhunan a jibge ba tare da mai su ba.
Da aka bincika buhunan sai aka ga sabbin takardun kudi 'yan dari bibbiyu da kuma hamsin-hamsin.
Sanarwar ta ce an fara bincike gadan-gadan domin gano masu safarar kudin.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewar an samu kudaden yau Talata, inda ya ce an fara bincike domin gano wadanda suka kai kudaden filin jirgin saman na Kaduna.
Ya kara da cewar kudaden ba na jabu bane.
Amman bai ce ko waye hukumar take zargi da aikata laifin safarar kudin ba.
Comments