Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sanar Da Hana Acaba Da Bara A Tituna Da Manyan Biranen Jihar
Gwamnati ta ce daga yau za’a kama duk wanda ya ke yin Acaba ko kuma aikata bara a manyan tinunan jihar.
Kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwan bayan taron kwamitin tsaron tsaron jihar da akayi a fadar gwamnatin jihar.
Sanarwan ta ce da ma can akwai dokar hana Acaba a jihar an dan daga kafa bne domin gwamnati ta gama wasu ayyuka da takeyi, amma daga yau an dakatar da hakan.
Comments