Bincike Ya Gano Alaka Tsakanin Kiba Da Cutar Daji (Cancer)

Masu bincike a Birtaniya, sun gano cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin Kiba da kuma cutar Sankara ko Cancer a turance.
Masu binciken kimiyyar na cibiyar Imperial College da ke birnin Landan sun ce, mutanen da suke da kiba sosai sun fi sirara hadarin kamuwa da samfurin cutar Kansa iri goma sha daya da suka hada da, kansar da ta shafi Ciki, da Hanta, da Tumbi, da Hanji, da kansar Mama da kuma ta Mahaifa.
An futar da sakamako fiye da 200 kan batun, wanda Birtaniya ta jagoranta, ya nuna alaka tsakanin cutar Kansa da kiba, sun karkare da cewa da zarar mutum ya fara narka kiba, to cutar Kansa na nan labe ta na jiran afka masa.
Kula da lafiyar jiki ta hanyar kiyaye narka kiba, da motsa jiki da rage shan taba sigari za su taimaka wajen hadarin kamuwa da cutar.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kiyasin kashi 40 cikin 100 na mutane a duk fadin duniya nauyinsu ya wuce kima, ya yin da kashi 13 cikin 40 su ke cikin hadarin kamuwa da narka kiba.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya