Wasu Taragai Sun Goce Daga Jirgin Kasa Da Ya Nufi Kano A Osogbo

Wadansu taragai na wani jirgin kasa da ya taso daga Legas zuwa Kano sun balle sun kuma goce daga kan layin dogo a wani hatsari da Allah Ya takaita.
Wannan lamari ya faru ne a garin Osogbo ta jihar Osun a ranar Asabar 4 ga watan Maris a cewar kamfanin dillancin labarai na najeriya NAN da jaridar Daily Nigerian ta rawito.

Labarin ya ci gab da cewa, taragan guda uku da ke makale da sauran taragun fasinja sun balle ne a daidai unguwar Ifon a Osun da misalin 1:45 na tsakar daren Asabar wayewar garin Lahadi.

Bayan ballewar taragan sai suka gangara da kansu zuwa wata mahadar layin dogon a wata tasha ta yankin Osogbo a inda kafar taragon ta zame daga kan layin dogon da suke kai, sanna kuma suka jirkice kasa.
Wani mai suna Biodun Opatoyinbi wanda lamarin ya faru a idonsa ya shaidawa NAN cewa, a saninsa babu wani wanda ya jijkkata illa wani mai suna Mista Yakubu wanda aka fi sani da Baba Ibeji da ya ke cikin taragun ne a lokacin da hadarin ya faru, kuma da alama bai ji ciwo ba.

Ya kuma ce, an samu nasarar tsayar da matukin jirgin ne wanda bai san abin da ya faru ba a garin Offa na jihar Kwara.

Sannan Biodun ya kuma ce, jami'an 'yan sanda sun cafke wani mutum da ya ke kokarin diban kayan cikin wasu taragan, yayin da jam'in rundunar tsaro na Civil Defence ke ci gaba da kulawa da kayayyakin taragan.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya