Yan Nigeria sun cika mita — Bincike

Wani bincike a baya-bayan nan,na cewa 'yan Nigeria na sahun gaba a tsakanin al'ummomin kasashen duniya da suka fi mita da korafi kan shugabanninsu.
Binciken wanda wata ƙungiyar bin diddigin mulkin dimokraɗiyya a duniya mai suna Good Governance Group ta fitar ya nanata buƙatar 'yan Nijeriya su sauya hali kan yadda suke kallon masu madafun iko da ma yadda gwamnati ke biyan buƙatunsu.
Wani masani kan Dr. Abdullahi Yelwa masanin kan zamantakewa da halayyar ɗan'adam ya ce 'yan Nijeriya suna kallon shugabanninsu a kowanne mataki mutane masu ci-da-guminsu da ke fake da sunan wakiltar al'umma suna azurta kansu da iyalansu.
Ana ganin rashin fahimtar gwamnati da kuma kaifin talauci sun taimaka wajen dusashe damar da 'yan ƙasar ke da ita ta ƙalubalantar shugabanninsu.
Haka zalika, matsalar ta janyo ƙaruwar tumasanci da barace-barace
Wani tsohon kantoman ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe, Alhaji Yusuf Yunusa ya ce jama'a ba sa tunkarar shugabanni da buƙatu ko matsalolin al'umma ɗungurungum sai dai na ɗaiɗaikunsu.
Ya ce idan ka yi ƙididdigar mutanen da suke zuwa ƙaramar hukuma, za ka ga mafi yawa suna zuwa ne da buƙatu irinsu "an yi min haihuwa da zan gyara rufin gida", amma ba wani abu zai amfani kowa da kowa ba.
Sai dai su kuma talakawan na cewa idan sun kai buƙatun al'umma, shugabannin ba sa magantawa, don haka sukan gwammace su je da ƙaramar buƙatarsu, don a sallame su nan take.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya