Jagoran Musulmi a India ya rasu
Daya daga cikin shugabannin Musulmi a kasar Indiya, Syed Sahhabuddin, ya rasu yana da shekara 82 a duniya bayan doguwar jinya, kuma tuni aka yi jana'izarsa daidai da koyarwar addinin musulunci.
Syed Shahabuddin jami'in difilomasiyya ne kana daga bisani ya zama dan siyasa.
Ya taka rawar gani wajen tabbatar da an haramta littafin nan mai suna The Satanic Verses , wanda marubucin adabi dan Birtaniya mai tsatson Indiya, Salman Rushdie, ya rubuta.
Littafin dai ya yi tsokaci ne a kan Annabi Muhammad (S.A.W), kuma Musulmi da dama na kallon littafin a matsayin sabo.
A shekarar 1988 aka haramta littafin a kasar Indiya, kuma ya zuwa yanzu ba a dage haramcin ba.
Marigayin ya kuma yi fice wajen gwagwarmayar hana mabiya addinin Hindu masu tsananin kishin kasa lalata masallacin Babri, wanda ke daya daga cikin manyan masallatai a kasar.
A 1985, ya kuma nuna adawa da wani hukunci da kotun koli ta yanke na tilasta wa miji kula da matarsa ko bayan mutuwar aurensu. Hukuncin dai ya kawo sauye-sauye a rayuwar al'uma muslmi a Indiya, wadanda kuma suka janyo cece-kuce.
An haifi Syed Shahabuddin a 1935 a Ranchi kasar Indiya. Ya dai yi suna a ciki da wajen kasar musamman a kasashen musulmi da kuma a kasashen yamma.
Mataimakin shugaban kasar, Hamid Ansari, a sakon ta'aziyyarsa, ya bayyana marigayi Syed Shahabuddin a matsyin mutum mai juriya, da kwazo da kuma dogewa kan abin da ya yi imani da shi.
Comments