Ana Zargin Tsohon Kwamishina A Kano Da Badakalar Dala $650,000
Ana zargin tsohon kwamishinan lafiya na jihar Kano, Abubakar Labaran, tsohon babban sakataren ma'aikatar lafiya, Farouk Mohammed, da tsohon shugaban kwalejin unguwar zoma ta jihar Kano, Tijjani Umar da tafka badakalar Dala $650,000,
Majiyar Hausa Times ta ruwaito cewa ana zarginsu da zambatar Gwamnatin jihar a karkashin shirin tallafin karo karatu a kasashen waje,
DailyNigerian ta ruwaito cewa mutanen sun hada kai ne da wani jami'in tuntuba dan kasar Misira, Thamer Kazamel, inda suka rubanya kudaden karatu ga daliban jihar Kano da aka tura karo karatu a jami'ar Mansoura dake Misira.
Kwamishinan da mukarrabansa sun yi sojan gona da wani kamfani, Medical Overseas Limited, a yayinda shi kuma jami'in tuntubar yayi amfani da kamfanin, Delta Med Group.
Tuni dai hukumomi a kasar Misira suka samu nasarar kwace Dala $200,000 daga Mista Thamer a yayinda tsohon shugaban makarantar unguwar zoman ya yi ikirarin ya karbi $94,000 ne kacal daga cikin kudin.
Majiyar ta Hausa Times ta tsegumta cewa Kawo yanzu an maido Dala $450,000 Nigeria a yayinda ake cigaba da binciken wadanda ake zargin.
Tuni dai mahukuntan suka sha alwashin mika wadanda ake zargin a gaban kuliya. A yayinda ake jiran hukumar EFFCC ta karbi kudaden ta mayar dasu asusun Gwamnatin jihar Kano.
Comments