Wata mata ta watsa wa mijinta ruwan zafi a mazakutarsa
Wata mata mai suna Kafayat ta watsa wa mijin ta ruwan zafi a mazakutarsa a garin Ibadan.
Mijin nata wanda malamin makaranta ne mai suna Adelakun ya maka matar tasa a Kotu ya na neman a warware auren nasu.
Ya fadi wa kotu cewa har yanzu ba zai iya amfani da mazakutarsa ba saboda konewa da tayi.
Ko da yake Kafayat tace tsautsayi ne ya sa hakan ya faru dai dai tana rike da ruwan zafi amma ba wai tayi da gangar bane.
Mijin nata dai ya umurci kotun da ta raba auren nasu domin ba zai iya zama da wannan mata ba.
Comments