Wanne hadari shan Fanta da Sprite ke da shi a Nigeria?
Wata sharia'a da aka yi a baya-bayan nan a wata kotun Najeriya, ta bayyana cewa akwai yiwuwar lemukan kwalaba da ake yi a kasar na da hadari ga mutane, kamar yadda Ijeoma Nduke ta bayyana a rahoton da ta hada.
Ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan da aka gano cewa wata kotu ta bai wa kamfanin da ke yin Fanta da Sprite na Nigeria bottling Company NBC, umarnin ya rika manna takardar da ke dauke da gargadi a kan lemukan da yake yi.
Kotun ta bukaci kamfanin ya yi wa mutane gargadi cewa shan lemun tare da kwayar maganin bitamin C na da hadari kwarai.
Masu suka na cewa lemukan na dauke da sinadarin benzoic acid da ya wuce kima da kuma kalar da ake sakawa.
Sai kamfanin hada lemukan na NBC yana kalubalantar hukuncin.
Lamarin ya jawo damuwa sosai a Najeriya, inda mutanen kasar da dama ke shan wadannan lemuka.
Barbara Ukpabi, wata mai gidan sayar da abinci ce kuma tana sayar da abincin gargajiya iri-iri a unguwar Oniru da ke jihar Legas.
Barbara ta ce akwai yiwuwar zata bar sayen Fanta da Sprite domin ta sayar a gidan sayar da abincinta, kuma ta na fargabar bai wa yaranta lemun.
"Da ina tunanin na rage yawan lemun da nake sha. Zan rage sha ko kuma na rika shan wasu lemukan dangin 'ya'yan itatuwa."
Amma shan irin wadannan lemukan, dabi'a ce mai wahalar bari ga 'yan Najeriya da dama.
"Yanzu nan na ci abincin rana kuma na sha lemon Coke da ruwa."
John Uloko, wani mai gadi ne, kuma bai ga rahoton da aka yi kan lemukan a jarida ba amma ya ji labari ta manhajar WhatsApp, kuma tun daga lokacin bai kara sha ba.
Me yasa aka yanke shawarar?
A shekarar 2007, Mista Adebo ya tafi da Fanta da Sprite din da aka yi Najeriya zuwa Ingila domin ya sayar da su a wasu shagunansa da ke barin Manchester.
Amma sai hukumar fasa kaurin Birtaniya ta rike masa kayan. Da farko sun rike kayan ne saboda suna shakku kan ingancin lemukan.
Amma da hukumomin lafiya na Burtaniya suka yi gwaji kan lemukan, sai aka tabbatar shan su na da hadari ga rayuwar dan adam, don haka aka lalata su.
Wannan dalilin ne yas a Mista Adebayo ya shigar da karar kamfanin yin lemukan na NBC reshen Najeriya, wadanda suka sayar masa da su.
Da farko dai kamfanin ya ki ya dauke wa Mista Adebayo asarar da ya yi.
Daga baya sai ya kai karar hukumar kula da abinci da ingancin magunguna ta Najeriya, NAFDAC, a kan cewa ba su yi aikinsu yadda ya kamata ba.
A watan da ya gabata ne kusan shekara goma bayan ya shigar da karar, wata babbar kotu a Legas ta bai wa kamfanin laifi kuma ta bukaci kamfanin NBC din ya rubuta gargadi a jikin robobin Fanta da Sprite.
A yayin da NBC ke daukaka karar, har yanzu bata fara manna gargadin jikin robobin lemukan ba.
Mista Adebayo ya shaidawa BBC cewa, "Da farko suna nuna isa kan lamarin, wanda hakan ya jawo aka bata lokaci. Na kai NAFDAC kotu domin ta tursasa mata ta yi aikinta.
"Bai dace a ce muna da kayayyakin abincin da a Turai ake ganin su a matsayin marasa inganci ba."
Mutane da dama sun amince da wannan ra'ayi na Mista Adebayo, inda suke bakin cikin cewar an halasta wa 'yan Najeriya cin abin da ake zaton yana da hadari ga rayuwar mutane, amma a hannu guda kuma an haramta a Burtaniya.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce a kan ingancin kayayyakin abinci a kasar.
Duk da cewa ana amfani da sinadarin benzoic wajen adana abinci da lemuka domin kara yawan kwanakin da za su iya yi ba tare da sun lalace ba, bincike ya gano cewa sinadarin na iya jawo rashin lafiya a wasu lokutan.
Wani masanin kimiya da ke aiki tare da NAFDAC a Najeriya, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce wani bincike da aka gudanar ya gano cewa sinadarin benzoic zai iya haifar da sinadarin benzene idan aka hada shi da sinadarin bitamin C.
Shan wannan hadin na iya jawo wa mutum cutar kansa ta jini da ma wasu cututtukan da suka shafi jinin.
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya, ta wallafa wata sanarwa a matsayin wani martani bayan da mutane suka fara korafi, inda suka kara tabbatar wa 'yan Najeriya cewa lemukan basu da wani hadari.
Duk da haka, ma'aikatar ta bayar da shawarar cewa an fi so a sha magani da ruwa ba da lemu ba saboda gujewa aukuwar wata tangarda.
Duk da cewa gwamnati bata kafa doka ba, tana karfafa gwiwar kamfanonin da suke hada lemu su rika rubuta gargadi suna mannawa a jikin robobin lemukan da suke samar wa.
Kamfani samar da lemuka na Nigeria Bottling Company da ke Najeriya ya daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke.
Ta ce sinadarin benzoic da suke sakawa a lemukansu bai wuce kima ba, kuma dai-dai yake da adadin da hukumar da ke saka ido kan abinci da magunguna ta Najeriya da takwararta, Codex Alimentarius suka kayyade.
Comments