Amarya Ta Haihu Bayan Kwana Biyu Da Daura Aure

Auren Zawarawa da 'yan mata 1,520 daga kananan hukumomin jihar Kano guda 44 da aka yi a ranar Lahadin ta gabata ya bar baya da kura yayin da daya daga cikin Amaren Habiba Inusa ta haifi da Namiji bayan kwana biyu da daura auren.
A cewar Habiba cikin na Angon nata ne Babangida. Duk da dai bai yi wata-wata ba ya gaggauta fatattakar ta daga gidansa.
Sai dai daga baya wanda ake zargi da yi mata cikin ya cika wandonsa da iska.
A yayin tuntubar kwamandan rundunar Hisbah na jihar Kano Malam Aminu Daurawa akan ikirarin da ya yi na cewa kowacce daga cikin Amaren an tantance lafiyar ta. Sai ya ce daga baya gwamnatin jihar Kano ta kwace abin daga wajen su ta damka shi ga ‘yan siyasa.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya