HOTUNA: An Bude Katafaren Masallacin Da Tsohon Shugaba Obasanjo Ya Gina
Tsohon shugaba Obasanjo ne dai ya gina katafaren masallachin da cibiyar addinin musulunci a garin Abeokuta. Kuma an bude shi ne yayin bikin cikarsa shekaru 80.
Bikin bude masallachin ya sami halartar manyan baki, kamar su mai martaba Ibrahim Sulu Gambari, Dan Kano da sauran manyan baki.
Daga karshe a ka gabatar da lacca daga bakin Sheikh Sulaiman Faruq Onikigipa.
Comments