An Yi Yunkurin Hallaka Sarkin Saudiyya A Malaysia

Hukumomin kasar Malaysia sun sanar da cewa sun dakile yunkurin hallaka sarki Salman bn Abdul'azeez na kasar Saudiyya a lokacin da ya kai ziyara kasar a baya-bayan nan.
Sufeton 'yan sandan kasar Khalid Abu Bakar shi ne ya sanar da hakan, ya kara da cewa gabannin kawo ziyarar, 'yan sanda sun cafke wasu mutane bakwai, cikin su har da wasu 'yan tawaye na kabilar Houthi a kasar Yemen.
Tun bayan guguwar sauyi ta hambarar da gwamnati shugaba Ali Abdallah Saleh, kasar Yemen ta fada tashin hankali, bayan wani lokaci aka zabi Abdul Rabou Mansul-Hadi a matsayin sabon shugaba, daga bisani shi sai da ya tsere zuwa Saudiya dan neman mafaka.
Shekaru biyu kenan da Saudiyya ke jagorantar wata hadakar dakarun kasashen waje, a yakin da suke yi da 'yan tawayen Houthi a Yemen.
Amma kawo yanzu babu tabbacin ko su 'yan Yemen din 'yan wacce kungiyar 'yan tawaye ne.
Wata babbar majiyar 'yan sanda ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar an yi imanin mutanen 'yan tawayen Houthi ne.
Amma wasu majiyoyin sun ce mutanen da ake tuhumar na da alaka da kungiyar IS.
Kuma babu tabbacin ko mutane ukun da aka kama 'yan kungiya daya ne.
An kama mutum bakwai din da ake tuhumar ne daga tsakanin ranar 21 zuwa 26 ga watan Fabrairu- ranar da Sarki Salman ya isa babban birnin Malaysia.
Babban hafsan 'yan sandan kasar, Khalid Abu Bakar, ya shaida wa manema labarai cewar kungiyoyin "na shirin kai hari ne kan sarkin da tawagarsa a lokacin ziyararsu zuwa Kuala Lumpur."
"Mun same su a kan lokaci," in ji shi.
'Yan sanda sun kuma kwace fasfunan da dama daga wadanda ake zargin, da kudi dala 60,740 na kudin kasashe daban-daban, wanda aka yi amanna an so tura su ne ga kungiyoyin masu tayar da kayar baya.
Mista Abu Bakar ya shaida wa 'yan jarida cewa, "kungiyar tana kuma tu'ammali da mugayen kwayoyi."
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a yanzu haka Yemen na fuskantar karancin abinci da ke bukatar taimakon gaggawa, inda aka yi kiyashin cewa mutum miliyan 7.3 ne suke bukatar agaji, yayin da mutum 10,000 suka rasa ransu tun farko rikicin.
Sarki Salman ya je ziyarar ne da tawagar 'yan rakiya kusan mutum 600 a kwanaki hudun da ya yi a Malaysia.
Wata tafiya ce da ya tsara don yin rangadi a yankin Asiya, inda ya tafi da kayan alatu da na alfarma.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARI: Amfanin Kabeji A Jikin Dan Adam

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

An sake gano dala miliyan 150 da aka sace a Najeriya