Posts

Showing posts from March, 2017

Yan Nigeria sun cika mita — Bincike

Image
Wani bincike a baya-bayan nan,na cewa 'yan Nigeria na sahun gaba a tsakanin al'ummomin kasashen duniya da suka fi mita da korafi kan shugabanninsu. Binciken wanda wata ƙungiyar bin diddigin mulkin dimokraɗiyya a duniya mai suna Good Governance Group ta fitar ya nanata buƙatar 'yan Nijeriya su sauya hali kan yadda suke kallon masu madafun iko da ma yadda gwamnati ke biyan buƙatunsu. Wani masani kan Dr. Abdullahi Yelwa masanin kan zamantakewa da halayyar ɗan'adam ya ce 'yan Nijeriya suna kallon shugabanninsu a kowanne mataki mutane masu ci-da-guminsu da ke fake da sunan wakiltar al'umma suna azurta kansu da iyalansu. Ana ganin rashin fahimtar gwamnati da kuma kaifin talauci sun taimaka wajen dusashe damar da 'yan ƙasar ke da ita ta ƙalubalantar shugabanninsu. Haka zalika, matsalar ta janyo ƙaruwar tumasanci da barace-barace Wani tsohon kantoman ƙaramar hukumar Nguru a jihar Yobe, Alhaji Yusuf Yunusa ya ce jama'a ba sa tunkarar shugabanni d...

Sunayen sababbin kwamishinonin hukumar zabe da Buhari ya aika majalisa

Image
Yau ne majalisar dattijai ta karanta sunayen mutane 27 da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika majalisar domin amincewa da su kwamishinonin zabe. Ga sunayen: 1. Godswill Obioma, Abia 2. Ibrahim Abdullahi, Adamawa 3. Ahmed Makama, Bauchi 4. James Apam, Benue 5. Mike Igibi, Delta 6. Nwachukwu Orji, Ebonyi 7. Iloh Chuks, Enugu 8. Hussaini Pai, FCT 9. Sadiq Musa, Kaduna 10. Jibrin Zarewa, Kano 11. Asmau Maikudi, Katsina 12. Mahmuda Isah Kebbi 13. Samuel Egwu, Kogi 14. Rufus Akeju, Lagos 15. Mustapha Zubairu, Niger 16. Agboke Olaleke, Ogun 17. Sam Olumekun, Ondo 18. Abdulganiyu Raji, Oyo 19. Riskuwa Shehu, Sokoto 20. Kasim Geidam, Yobe 21. Bello Mahmud, Zamfara 22. Nentawe Yilwada, Plateau 23. Umar Ibrahim, Taraba 24. Emeka Joseph, Imo 25. Obo Effanga, Cross River 26. Francis Ezeonu, Anambra da 27. Briyai Frankland, Bayelsa

Wata mata ta watsa wa mijinta ruwan zafi a mazakutarsa

Image
Wata mata mai suna Kafayat ta watsa wa mijin ta ruwan zafi a mazakutarsa a garin Ibadan. Mijin nata wanda malamin makaranta ne mai suna Adelakun ya maka matar tasa a Kotu ya na neman a warware auren nasu. Ya fadi wa kotu cewa har yanzu ba zai iya amfani da mazakutarsa ba saboda konewa da tayi. Ko da yake Kafayat tace tsautsayi ne ya sa hakan ya faru dai dai tana rike da ruwan zafi amma ba wai tayi da gangar bane. Mijin nata dai ya umurci kotun da ta raba auren nasu domin ba zai iya zama da wannan mata ba.

Wanne hadari shan Fanta da Sprite ke da shi a Nigeria?

Image
Wata sharia'a da aka yi a baya-bayan nan a wata kotun Najeriya, ta bayyana cewa akwai yiwuwar lemukan kwalaba da ake yi a kasar na da hadari ga mutane, kamar yadda Ijeoma Nduke ta bayyana a rahoton da ta hada. Ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan da aka gano cewa wata kotu ta bai wa kamfanin da ke yin Fanta da Sprite na Nigeria bottling Company NBC, umarnin ya rika manna takardar da ke dauke da gargadi a kan lemukan da yake yi. Kotun ta bukaci kamfanin ya yi wa mutane gargadi cewa shan lemun tare da kwayar maganin bitamin C na da hadari kwarai. Masu suka na cewa lemukan na dauke da sinadarin benzoic acid da ya wuce kima da kuma kalar da ake sakawa. Sai kamfanin hada lemukan na NBC yana kalubalantar hukuncin. Lamarin ya jawo damuwa sosai a Najeriya, inda mutanen kasar da dama ke shan wadannan lemuka. Barbara Ukpabi, wata mai gidan sayar da abinci ce kuma tana sayar da abincin gargajiya iri-iri a unguwar Oniru da ke jihar Legas. Barbara ta ce akwai yiwuwar zata bar sayen Fanta ...

An samu naira miliyan 49 jibge a filin jirgin sama na Kaduna

Image
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) ta ce ta samu naira miliayan 49 a jibge a filin jirgin sama na Kaduna da ke arewacin kasar. Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce jami'anta sun kama kudaden cikin manyan buhuna biyar. Sanarwar ta ce an gane kudaden ne a lokacin da ake bincika kayayyakin matafiya kuma aka ga buhunan a jibge ba tare da mai su ba. Da aka bincika buhunan sai aka ga sabbin takardun kudi 'yan dari bibbiyu da kuma hamsin-hamsin. Sanarwar ta ce an fara bincike gadan-gadan domin gano masu safarar kudin. Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewar an samu kudaden yau Talata, inda ya ce an fara bincike domin gano wadanda suka kai kudaden filin jirgin saman na Kaduna. Ya kara da cewar kudaden ba na jabu bane. Amman bai ce ko waye hukumar take zargi da aikata laifin safarar kudin ba.

Dillalan Motoci Dokarmu Za Ta Shafa — Kwastam

Image
Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Najeriya wato Kwastam, ta ce ba a fahimci dokar da take son aiwatarwa ba dangane da batun karbar harajin shiga da mota kasar. Hukumar ta ce dokar ba ta nufin bincikar duk wanda ke da mota a kasar domin ganin ko ya biya kudin fito ko bai biya ba. Mataimakin shugaban hukumar ta Kwastam, Aminu Abubakar Dan Galadima, ya ce "Dokar za ta yi aiki ne kawai kan dillalan motocin da suka shigo da sabbin motoci cikin kasar ba tare da sun biya kudin fiton ba." Ya kuma ce babu haraji kan motocin da suka wuce shekaru takwas da kirkira. Sai dai kuma hukumar ta ce har yanzu tana kan bakarta ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasa. Ga dai yadda hirar ta kasance tsakanin Abdou Halilu na BBC da Aminu Abubakar Dan Galadima: Hukumar dai ta bayar da wa'adin wata guda domin fara aiwatar da wannan doka, al'amarin da ya sanya Majalisar Dattawan kasar ta yi wa shugaban hukumar kiranye. A ranar Litinin kuma shugaban hukumar, Hameed Ali, ya bayyana a gaban ...

Lauyan Bogi Ya Fashe Da Kuka Bayan Da Kotun Shariar Musulunci Da Ke Kurna A Kano Ta Damke Shi

Image

An Kama Karuwai Da Yan Kwaya 120 A Hills And Valley Da Ke Kano

Image
Kungiyar Hisba a jihar Kano ta sanar da kama ‘yan mata karuwai 79 da maza masu shaye-shaye 39 a wani gidan holewa mai suna Hills and Valleys Recreational Centre dake Awakin Kudu a jihar Kano. Shugaban Hisba a jihar Abba Sufi yace mata 20 daga cikin wadanda aka kama basu wuce shekara 13 zuwa 14. Yanzu dai za’a kaisu kotu domin yanke musu tara da kuma hora su.

Gwamna Umar Bindow Na Jihar Adamawa Ya Ziyarci Tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Danfulani Baba Suntai Da Ke Fama Da Rashin Lafiya Tun Hatsarin Jirgin Da Ya Yi A Shekarar 2012.

Image

HOTUNA: A yau Alhamis, 9 ga watan Maris, shugaba Buhari ya karbi bakuncin Archbishop of Canterbury, Rev Justin Welby. Ya karbe shi ne a Abuja House da ke birnin London.

Image

Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yake yi - Dr Martins Adejo

Image
Wani likita a asibitin Makurdi Dr Martins Adejo ya gargadi mata da su yi taka tsantsan da saka takalman masu tsini domin ya na lahanta kashin bayan mutum. Likitan yace wadannan takalma na illata kashin baya wanda hakan ya kan lalata wasu sassan dake hade da kashin baya bayan illata kashin shi kansa. Ya kara da cewa takalma masu tsini na kawo matsala a kwiwwowi da gabobi da tafin kafa, sannan kuma yana raunana jijiyoyin dake tafiyar da jinni a jikin mutum. “ Idan mace ta nace da sa irin wadannan talkalma za ta samu matsala da jijiyoyin ta da kuma gabobin jikinta idan girma ya zo. Likita Adejo yace dalilin irin wadannan matsaloli da za’a iya samu zai iya kai ga mutum ya kamu da cutar hawan jinni da ciwon suga.

HOTUNA: Rotimi Amaechi, Lai Mohammed, Kemi Adeosun na daga cikin ministocin da su ka halarci bikin taya  mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, murnar cika shekara 60.

Image

Bankuna 3 Sun Kwace Kamfanin Sadarwa Na ETISALAT

Image
Bankunan Guarantee Trust, Zenith da Access na shirin kwace kamfanin sadarwa ta Etisalat saboda bashin biliyoyin naira da take bin Kamfanin. Bankunan na bin kamfanin Etisalat bashin sama da naira biliyan N540. Kamfanin Etisalata na da masu amfani da layinta sama da mutane miliyan 21 a wata kididdiga da akayi a watan Janairun 2017. Kamfanin ta koka da tabarbarewan tattalin arzikin kasa a matsayin dalilan da ya sa kamfanin ta gagara biyan basussukan. Wani babban darekta a hukumar NCC yace hukumar ta yardan ma bankunan da su kwace kamfanin a matsayin bashinsu.

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sanar Da Hana Acaba Da Bara A Tituna Da Manyan Biranen Jihar

Image
Gwamnati ta ce daga yau za’a kama duk wanda ya ke yin Acaba ko kuma aikata bara a manyan tinunan jihar. Kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwan bayan taron kwamitin tsaron tsaron jihar da akayi a fadar gwamnatin jihar. Sanarwan ta ce da ma can akwai dokar hana Acaba a jihar an dan daga kafa bne domin gwamnati ta gama wasu ayyuka da takeyi, amma daga yau an dakatar da hakan.

An Yi Yunkurin Hallaka Sarkin Saudiyya A Malaysia

Image
Hukumomin kasar Malaysia sun sanar da cewa sun dakile yunkurin hallaka sarki Salman bn Abdul'azeez na kasar Saudiyya a lokacin da ya kai ziyara kasar a baya-bayan nan. Sufeton 'yan sandan kasar Khalid Abu Bakar shi ne ya sanar da hakan, ya kara da cewa gabannin kawo ziyarar, 'yan sanda sun cafke wasu mutane bakwai, cikin su har da wasu 'yan tawaye na kabilar Houthi a kasar Yemen. Tun bayan guguwar sauyi ta hambarar da gwamnati shugaba Ali Abdallah Saleh, kasar Yemen ta fada tashin hankali, bayan wani lokaci aka zabi Abdul Rabou Mansul-Hadi a matsayin sabon shugaba, daga bisani shi sai da ya tsere zuwa Saudiya dan neman mafaka. Shekaru biyu kenan da Saudiyya ke jagorantar wata hadakar dakarun kasashen waje, a yakin da suke yi da 'yan tawayen Houthi a Yemen. Amma kawo yanzu babu tabbacin ko su 'yan Yemen din 'yan wacce kungiyar 'yan tawaye ne. Wata babbar majiyar 'yan sanda ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar an yi imanin mu...

An Saki Mawakin Nan Na Kano, Sadiq Zazzabi

Image
An gurfanar da Zazzabi a kan ya saki wata waka akan tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso, ba tare da bin ka’idar cibiyar sakin wakoki da bidiyo ba. A yau Litinin, an bashi belin akan sharudda 3: Kudi N100,000, wani mamban kungiyar marubutan wakan jihar Kano, da kuma wani ma’aikacin gwamnati wanda ya kai akalla matsayi na 14. Ya cika sharuddan belin kuma an sake shi kuma an dakatar da karar zuwa ranan 27 ga watan Maris. Zazzabi yace an tsare shi ne saboda cewa shi masoyin tsohon gwamna Kwankwaso ne. Yayinda yake Magana da jaridar Premium Times, shugaban hukumar, Ismaila Afakallahu, ya tabbatar da cewa an sake shi.

Za A Iya Samun Gidan Yankan Kai A Kano — Ganduje

Image
Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce birnin Kano na fama da matsalar satar kananan yara. Satar yara kanana dai ta yi kamari a birnin na Kano a 'yan watannin da suka gabata musamman a wasu sassan gabashin birnin. Hakan ne kuma ya sanya sanya mazauna yankunan gudanar da zanga-zanga domin jan hankalin gwamnati ta dauki matakin shawo kan matsalar. To sai dai gwamna Ganduje ya ce yanzu haka suna kokarin shan kan matsalar nan ba da jimawa ba. Ya kuma amsa tambaya kan shin ko akwai gidan yankan kai a Kano? Ku saurari hirar gwamnan na Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a inda ya yi wa wakilin BBC, Yusuf Ibrahim Yakasai, karin bayani kan batun

Wasu Taragai Sun Goce Daga Jirgin Kasa Da Ya Nufi Kano A Osogbo

Image
Wadansu taragai na wani jirgin kasa da ya taso daga Legas zuwa Kano sun balle sun kuma goce daga kan layin dogo a wani hatsari da Allah Ya takaita. Wannan lamari ya faru ne a garin Osogbo ta jihar Osun a ranar Asabar 4 ga watan Maris a cewar kamfanin dillancin labarai na najeriya NAN da jaridar Daily Nigerian ta rawito. Labarin ya ci gab da cewa, taragan guda uku da ke makale da sauran taragun fasinja sun balle ne a daidai unguwar Ifon a Osun da misalin 1:45 na tsakar daren Asabar wayewar garin Lahadi. Bayan ballewar taragan sai suka gangara da kansu zuwa wata mahadar layin dogon a wata tasha ta yankin Osogbo a inda kafar taragon ta zame daga kan layin dogon da suke kai, sanna kuma suka jirkice kasa. Wani mai suna Biodun Opatoyinbi wanda lamarin ya faru a idonsa ya shaidawa NAN cewa, a saninsa babu wani wanda ya jijkkata illa wani mai suna Mista Yakubu wanda aka fi sani da Baba Ibeji da ya ke cikin taragun ne a lokacin da hadarin ya faru, kuma da alama bai ji ciwo ba. Ya kuma ce, ...

MABIYA SHI,A ZA SU GURFANAR DA GWAMNA GANDUJE A KOTU

Image
Jagoran Mabiya Shi'a a Kano Dakta Sanusi Abdulkadir Koki ya bayyana cewa sun kammala shirin su na gurfanar da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya bisa zarginsa da hada kai da hukumar 'Yan sanda aka kai musu hari a yayin tafiyarsu garin Zariya kimanin kwanaki dari da suka gabata. 'Yan shi'an sun bayyana cewa kimanin mutane 27 aka kashe musu tare da cafke 54 ciki hada mata da kananan yara. Dr. Sanusi Abdulkadir Koki ya kuma kara da cewa a yayin gabatar da karar za su hada da kwamishinan 'Yan sanda wanda da shi aka yi amfani wajan cin zalinsu ba tare hakkinsu ba. Haka kuma ya tabbatar da cewa za su shigar da wata karar a kotun Duniya Ta I.C.C da nufin bin kadin hukuncin da Kotu ta yanke ga shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky kan a sake shi, tare kuma da biyansa diyya. Amma kuma gwamnatin tarayya ta ki bin umarnin kotu kamar yadda ya bayyana. Daga karshe ya shedawa manema labaran cewa a yanzu suna yin addu'a tukuru kan Allah ya bi musu hakkinsu. ...

Shugaba Buhari Ya Kira Obasanjo Da Gwamnan Kogi

Image
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga kasar Ingila domin tayi shi murnan zagayowar ranar haihuwarsa yau. An gudanar da bukin zagayowar ranar haihuwar Obasanjo yau a garin Abeokuta da kaddamar wata sabuwar dakin karatu da ya gina. Buhari ya yabi Obasanjo kan irin shugabanci nagari da yayi musu a lokacin da suke aiki soji. Bayan haka Buhari ya kira gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Buhari yayi masa fatan alkhairi sannan ya ce masa lallai yana samun sauki kuma ya kusa dawo wa kasa Najeriya domin ci gaba da aiki. Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo bai yi kasa kasa ba wajen yaba ma Buhari da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya. Obasanjo yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai bashi kunya ba tun da ga ranar da ya hau kujeran mulkin kasa Najeriya har zuwa yanzu. Obasanjo yace a sanin Buhari da yayi tuntuni ba mutum bane da yake da amsoshi sosai ga yadda za’a bunkasa tattalin arzikin kasa, amma yayi matukar canzawa yanzu domin ana...

Najeriya Za Ta Wadata Da Shinkafa Kafin Karshen 2018 - Ogbeh

Image
Ministan lura da ayyukan noma da raya karkara na Najeriya, Chief Audu Obeh, ya ce kafin isa karshen shekara ta 2018 Najeriya zata dogara da kanta wajen noman shinkafa. Chief Ogbeh ya bada tabbacin ne, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, a garin Abuja, inda yace hakan na da nasaba da yadda manoma a kasar suka rungumi shirin gwamnati na karfafa noma a kasar. Ministan ya ce tuni gwamnatin kasar, ta shigo da manyan injinan tsaftace shinkafa sama da dari da goma, kuma nan bada dewaba za’a rarraba su zuwa inda ake bukata a sassan kasar.

HOTUNA: An Bude Katafaren Masallacin Da Tsohon Shugaba Obasanjo Ya Gina

Image
Tsohon shugaba Obasanjo ne dai ya gina katafaren masallachin da cibiyar addinin musulunci a garin Abeokuta. Kuma an bude shi ne yayin bikin cikarsa shekaru 80. Bikin bude masallachin ya sami halartar manyan baki, kamar su mai martaba Ibrahim Sulu Gambari, Dan Kano da sauran manyan baki. Daga karshe a ka gabatar da lacca daga bakin Sheikh Sulaiman Faruq Onikigipa.

Na Kama Matata Da Tsohon Mijinta A Kan Gadona Karara

Image
Wani magidanci mai suna Gbenga Akinade ya sanar da kotu cewa ya kama matarsa akan gadonsu na aure tare da tsohon mijinta suna aikata lalata karara. Gbenga ya roki kotu da ta warware wannan aure nasu. Ya ce dalilin haka ba zai iya ci gaba da zama da ita ba. Ya ce ko a lokacin da ya aure ta bai san cewa ita bazawara ce kuma ta na da ‘ya’ya biyu duk ya dauka budurwa ce. Gbenga yace a lokacin da suka hadu ta na sana’ar siyar da maganin garjiya wanda ake kira Agbo-jegi da yarban ci. Ya kuma ce ya fara ganewa ta na aikata irin wannan aiki ne bayan haihuwar ta na biyu da shi. “Busayo ta kan bar gida har na tsawo kwanaki biyu zuwa uku inda ta kan kai ‘ya’yan mu makwabta.” Akinade yace a ranar da ya kama ta da tsohon mijin na ta suna lalata ya yi ma ta dan karan duka amma yace bai daki tsohon mijin ba domin ya san idan hakan ya faru abin zai yi muni. Ya roki kotu da ta warware aurensu kuma ta bashi ikon rike ‘ya’yan da suka haifa tare...

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wurin bikin cikar Obasanjo shekaru 80

Image

Jagoran Musulmi a India ya rasu

Image
Daya daga cikin shugabannin Musulmi a kasar Indiya, Syed Sahhabuddin, ya rasu yana da shekara 82 a duniya bayan doguwar jinya, kuma tuni aka yi jana'izarsa daidai da koyarwar addinin musulunci. Syed Shahabuddin jami'in difilomasiyya ne kana daga bisani ya zama dan siyasa. Ya taka rawar gani wajen tabbatar da an haramta littafin nan mai suna The Satanic Verses , wanda marubucin adabi dan Birtaniya mai tsatson Indiya, Salman Rushdie, ya rubuta. Littafin dai ya yi tsokaci ne a kan Annabi Muhammad (S.A.W), kuma Musulmi da dama na kallon littafin a matsayin sabo. A shekarar 1988 aka haramta littafin a kasar Indiya, kuma ya zuwa yanzu ba a dage haramcin ba. Marigayin ya kuma yi fice wajen gwagwarmayar hana mabiya addinin Hindu masu tsananin kishin kasa lalata masallacin Babri, wanda ke daya daga cikin manyan masallatai a kasar. A 1985, ya kuma nuna adawa da wani hukunci da kotun koli ta yanke na tilasta wa miji kula da matarsa ko bayan mutuwar aurensu. Hukuncin dai ya kawo sauy...

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran manyan baki sun halarci bikin nadin Farfesa James Ayatse a matsayin Tor Tiv na 5

Image
Nadin Tor Tiv din dai na zuwa ne bayan rasuwar margayi Tor Tiv na Hudu, mai martaba Alfred Akawe Torkula. Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom shine ya jagoranci mika sandar girma ga sabon basaraken domin kama aiki. Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin nadin sarautar sun hada da sarakunan gargajiya da Kakakin majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Rt Hon Yakubu Dogara, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, A wata sanarwa da Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai ya fitar yace akwai kuma wakilan Gwamnonin Zamfara, Borno, Sokoto, Kebbi, Kogi, Jigawa, Plateau, Taraba da Kwara da kuma ministoci da yan majalisu da dai sauran manyan baki.

HOTUNA: Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Da Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, Wajen Taron Taya Olusegun Obasanjo Cika Shekara 80, Da A Ke Yi Yanzu Haka A Abeokuta

Image
Su biyun sun sauka a garin na Abeokuta ne tare, wajen katafaren bikin da aka shirya na murnar cikar tsohon shugaban kasa Obasanjo. A cikin bikin ne dai ake sa ran tsohon shugaban zai bude wani katafaren masallaci da ya gina.

HOTUNA: Yadda Aka Karbi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso A Enugu

Image
A jiya sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauka garin Enugu domin ya tattauna da gwamnan jihar da ke shirin rushe kasuwar shanu da ke jihar. 'Yan arewa ne dai ke kasuwanci tsawon lokaci a kasuwar. An yi wa tsohon gwamnan babbar tarba daga jama'ar jihar.

Karuwai Na Zanga-zangar Neman Halatta Karuwanci A Ukraine

Image
Karuwai da dama ne tare da ‘yan rajin kare hakkinsu suka fito suna zanga-zanga a yau Juma’a kan bukatar halatta karuwanci a Ukraine bayan gwamnatin kasar ta kafa dokoki masu tsauri da suka hada da cin tara ga masu sana’ar karuwanci. Karuwan na zanga-zangar ne a Kiev babban birnin Ukraine inda suka rufe fuska dauke da takardun da ke cewa “Karuwanci Sana’a ce, muna adawa da haramta Karuwanci”. Masu rajin kare hakkin Karuwan kimanin 50 ne rahotanni suka ce sun fito zanga-zangar inda suka mamaye ginin Majalisa a Kiev. Ukraine dai ta haramta sana’ar karuwanci, tare da karbar kudade tara kimanin dala 9 ga karuwan. Amma Karuwan sun ce suna iya biyan haraji maimakon tara da haramta sana’arsu. ‘Yan rajin kare hakkin Karuwan sun ce ‘Yan sanda na fakewa da dokar suna cin zarafin karuwan tare da karbar kudi a hannunsu.

Amarya Ta Haihu Bayan Kwana Biyu Da Daura Aure

Image
Auren Zawarawa da 'yan mata 1,520 daga kananan hukumomin jihar Kano guda 44 da aka yi a ranar Lahadin ta gabata ya bar baya da kura yayin da daya daga cikin Amaren Habiba Inusa ta haifi da Namiji bayan kwana biyu da daura auren. A cewar Habiba cikin na Angon nata ne Babangida. Duk da dai bai yi wata-wata ba ya gaggauta fatattakar ta daga gidansa. Sai dai daga baya wanda ake zargi da yi mata cikin ya cika wandonsa da iska. A yayin tuntubar kwamandan rundunar Hisbah na jihar Kano Malam Aminu Daurawa akan ikirarin da ya yi na cewa kowacce daga cikin Amaren an tantance lafiyar ta. Sai ya ce daga baya gwamnatin jihar Kano ta kwace abin daga wajen su ta damka shi ga ‘yan siyasa.

Buhari Ya Zanta Da Sarkin Morocco Ta Wayar Tarho

Image
Sarki Mohammed na shida na Morocco ya tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta tarho a London inda da ake diba lafiyarsa. Kakakin shugaban na Najeriya Femi Adeshina ya fadi a cikin sanarwar da ya fitar a yau Alhamis cewa Sarkin Morocco ne ya bukaci yin tattaunawar da Buhari. Sanarwar ta ce Sarkin na Morocco ya tambayi lafiyar Buhari tare da bayyana gamsuwarsa. Shugabannin sun kuma tattauna akan halin da ake ciki ga aikin shinfida bututun da zai ratsa Morocco zuwa kasashen Turai daga Najeriya. Sannan Sarkin ya sanar da Buhari game da bukatar Morocco na shiga kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS tare da mika godiya ga goyon bayan da suka samu na dawo da kasar a Kungiyar Tarayyar Afrika.