Yarinyar da 'bishiya' ke tsiro a jikinta
Lokacin da wani tsiro mai kama da ɓawon bishiya ya fara bayyana a fuskar wata yarinya 'yar shekara 10 Sahana Khatun wata huɗu da ya wuce, mahaifinta bai damu ba. Sai dai bayan sun fara yaɗo, ya damu matuƙa, inda ya tafi kudu da ƙauyensu zuwa Dhaka babban birnin Bangladesh don neman magani. Yanzu likitoci na fargabar cewa Sahana ka iya zama mace ta farko da ta taɓa fuskantar abin da ake kira "larurar tsirowar bishiya a jiki". Idan gwajin da suka yi ya tabbata, yarinyar ta shiga rukunin wasu mutane 'yan ƙalilan a faɗin duniya da ke fama da wannan larura mai suna epidermodysplasia verruciformis. Wasu mutane ƙalilan - duka maza ne- ake tsammanin suna da wannan cuta. Ga wasu mutanen, har ta ci ƙarfinsu, inda wani mutum ba ma ya iya taɓa mata da ɗansa tsawon shekara goma kenan. Hannuwan Abul Bajandar duk wani tsiro ya fito musu inda suka yi girman kilogram biyar, ga kuma wani tofo a ƙafafuwansa, idan ka gan shi tamkar bish...