Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi, ya ce dokar da yake son bujuro da ita kan aure a jihar ba gudu babu ja da baya. Sarkin wanda ya tabbatar da hakan, yayin jawabi a lokacin auren zawara 1500 da gwamnatin jihar Kanon ta gudanar, ranar Lahadi, ya ce, dokokin auren ne kawai za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye al'umma. Sarki Sunusi ya kawo wani misali dangane da yadda marasa karfi kan yi aure su kuma hayayyafa ba tare da kula da yaran nasu ba. "Wata mace ta kawo min karar mijinta cewa ya sake ta alhali suna da yara 10 tare saboda haka tana son a ja hankalin mijin nata wajen daukar nauyin yara guda bakwai, a inda ita kuma za ta kula da sauran ukun." In ji Sarki Sunusi. Ya kara da cewa "sai na kirawo mijin na fada masa korafin tsohuwar matar tasa, a inda ya ce min ai yana da wata matar kuma suna da 'ya'ya takwas, ka ga ke nan yana da yara 18 shi kadai." Sarki ya ce " ya tambayi sana'ar mutumin, a inda ya ce masa sana...